logo

HAUSA

UNHCR: Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijirar Najeriya 12,000 a bana

2023-12-22 20:53:22 CMG Hausa

Hukumar lura da ‘yan gudun hijira ta MDD ko UNHCR, ta ce kasar Kamaru ta karbi ‘yan gudun hijira 12,000 daga tarayyar Najeriya a shekarar nan ta 2023.

Wata sanarwa da UNHCR ta fitar a jiya Alhamis, ta ce sansanin ‘yan gudun hijira na Minawao, dake matsayin daya tilo a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru, a hukumance ya karbi ‘yan Najeriya 70,000 dake neman mafaka, bayan fuskantar tashe tashen hankula a yankunan su na asali.

Wakilin UNHCR a Kamaru Olivier Beer, ya shaidawa wani taron manema labarai a birnin Yaounde fadar mulkin Kamaru, cewa karuwar sabbin mazu zuwa sansanin na iya cika shi sama da kima, don haka akwai bukatar warware wannan matsala, ciki har da gaggauta mayar da wasu daga ‘yan gudun hijirar gida bisa radin kan su.

Mista Beer ya ce "Akwai kimanin ‘yan gudun hijira 14,000 dake fatan komawa gida. A shekara mai zuwa, za mu yi kira da a gudanar da taron sassa 3, wato Najeriya da Kamaru da UNHCR, domin fara laluben hanyoyin mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gida”.   (Saminu Alhassan)