Angola ta sanar da ficewa daga kungiyar OPEC
2023-12-22 09:21:46 CMG Hausa
Gwamnatin kasar Angola ta sanar a shafinta na Facebook cewa, ta fice daga kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.
Matakin Angola na ficewa daga kungiyar, ya biyo bayan zaman majalisar ministocin kasar da aka yi a jiya Alhamis a fadar shugaban kasa da ke Luanda, babban birnin kasar.
Ministan albarkatun ma'adinai, mai da iskar gas na kasar, Diamantino Pedro Azevedo, ya shaidawa manema labarai cewa, a halin yanzu Angola na ganin ba ta samun komai a cikin kungiyar, wannan ya sa ta dauki wannan mataki domin ta kare muradunta.
Angola na daya daga cikin manyan kasashen da ke fitar da mai a yankin kudu da hamadar Sahara.(Ibrahim)