logo

HAUSA

Majalissar wakilan tarayyar Najeriya ta bukaci da a fara amfani da kudin Yuan na kasar Sin a matsayin kudin musaya a kasar

2023-12-21 09:19:46 CMG Hausa

Majalissar wakilan tarayyar Najeriya ta bukaci kwamitinta mai lura da harkokin bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade da ya hada kai da babban bankin kasa na CBN domin fito da tsare-tsaren da suka dacewa wajen tabbatar da ganin an fara amfani da manufar 2018 da ya bayar da damar amfani da kudin Yuan na kasar Sin a matsayin kudin musaya da kasashen ketare.  

Majalissar ta zartar da wannan shawara ce, biyo bayan kudurin da dan majalissa Hon Jafaru Gambo Leko daga jihar Bauchi ya gabatar yayin zaman majalissar, inda majalissar ta ce komawa amfani da kudin kasar Sin zai taimaka wajen dakile karyewar darajar Naira a Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Da yake gabatar da kudurin, Hon Jafaru Gambo Leko ya ce, bisa la’akari da adadin yawan cinikayyar dake wakana tsakanin Najeriya da kasar China, ya dace matuka kudin kasar Sin su kasance cikin kudaden musaya da Najeriya za ta rinka amfani da su a harkokin kasuwancin kasa da kasa.

Bayan kammala zaman majalissar kuma, Hon Jafaru Gambo Leko ya yi wa manema labarai karin haske a game da kudurin da ya gabatar wanda kuma ya sami karbuwa a zauren majalissar.

“Muna da lamari na kasuwanci da kasar China fiye da Amerika, Amerika in ka duba bai kai kashi 10 ko 12 ba, mu’amalarmu na shigowa da fitar da kayayyaki, amma kuma sai ka duba yanzu a Najeriya ban da abinci da magani, ba abin da ake nema kamar dala. Mu kuma ga halin da ’yan kasuwanmu duka daga Arewaci da Kudanci da ko’ina sun fi kawo kaya daga kasar China, yanzu idan ka duba ko a gidanka in ka duba za ka samu, ko a nan ofishi na akwai abubuwa sun fi 10 wanda daga China aka yi su. Saboda haka wannan kuduri mun kawo ne don kowa dala yake nema, idan aka zo aka fara amfani da wannan kudi na China, in Allah ya yarda nema dala zai ragu. Sabo da haka, karfin Naira kuma zai dawo. Na farko ba wani ne zai zo ya gyara maka gidanka ba, kai ya kamata ka gyara. Za ka duba ne na farko ba wani kasa za ka duba ba, al’ummar kasarka za ka duba. Me suke bukata? Me ya kamata ka yi masu? Menene damuwarsu? Bai kamata a ce don muna tsoron Amerika za ta yi wani abu ba, ai mu ma kasa ne kuma masu ’yancin kai, kuma mu ’yan majalissa ne, kuma muna majalissar nan ne saboda talakawanmu ne, saboda haka ba wai za a ji tsoron wani abu ba ne, ai mun zama muna da ’yanci. Idan kuma muna tunanin sai abun da wata kasa ta ce to ya zama ba mu da ’yanci ke nan, za mu yi don talakan Najeriya abun da muke nema shi ne talakawan Najeriya su ba mu goyon baya. Wannan abu ya tabbata. Ni ba a nan zai tsaya ba har shi ambasadan China za mu je mu zauna da shi a matsayina na dan majalissa da sauran ’yan majalissa wanda suka ba ni goyon baya a cikin zauran majalissa. Za mu je mu zauna tun da damuwarmu Najeriya ne mu ga yaya za a yi, su fara shigo mana da kudin China kasar nan don a samu saukin mu’amalar kasuwanci.” (Garba Abdullahi Bagwai)