logo

HAUSA

An tsawaita kada kuri'a a zaben gama-gari a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo

2023-12-21 10:28:53 CMG Hausa

Hukumar zabe mai zaman kanta a Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo (DRC) wato CENI, ta sanar da cewa, za a ci gaba da kada kuri'a a babban zaben kasar. 

Kimanin masu kada kuri'a miliyan 44 aka yi wa rajista a kasar, inda za su zabi sabon shugaban kasa, da ’yan majalisar dokoki da na larduna, da kansilolin kananan hukumomi a zaben na jiya, amma da dama daga cikin rumfunan zabe, ba su samu damar budewa a kan lokaci ba, saboda wasu ’yan matsaloli. Haka kuma an samu rahotannin tashin hankali nan da can.

’Yan takara biyar dake neman kujerar shugabancin kasar, sun bukaci a shirya wani sabon zabe tare da sabon ofishin CENI.

A cewar tawagar CENCO da majami’ar Christ in Congo (ECC) wadanda ke sanya ido kan zaben, kashi 31.37 na rumfunan zabe a fadin kasar, ba su bude a kan lokaci ba. (Ibrahim Yaya)