logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta sanar da yin tafiye-tafiye kyauta ta jiragen kasa ga ’yan kasar a lokutan Kirsimeti da sabuwar shekara

2023-12-21 10:28:47 CMG Hausa

Gwamnatin Najeriya ta sanar da wani shiri na yin tafiye-tafiye ta jiragen kasa kyauta da kuma rage farashin sufuri da kaso 50 bisa 100 na motocin safa-safa na alfarma a tituna 22 a fadin kasar, a wani mataki na sassauta matsalar rashin kudi, dake da alaka da hutu, da tafiye-tafiye a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara.

Ministan raya ma’adinai na kasar Dele Alake, ya shaidawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, manufar matakin da gwamnati ta dauka na rage farashin sufuri ga jama'a, ita ce ba da dama ga matafiya na cikin gida, su ziyarci ’yan uwan da garuruwansu, ba tare da damuwa da karin nauyi da tsadar sufuri ya sanya a wadannan lokuta ba.

Ya ce, gwamnati za ta hada kai da masu motocin sufuri, da kungiyoyin direbobi na kasa, da kuma hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya, domin ganin an aiwatar da shirin da shugaban kasar ya bullo da shi, ba tare da wata matsala ba. (Ibrahim Yaya)