logo

HAUSA

Birnin Chengdu na Sin zai karbi bakuncin gasar nau’o’in wasannin lankwasa jiki ta duniya ta 2027

2023-12-20 21:17:31 CRI

Birnin Chengdu fadar mulkin lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin, zai karbi bakuncin gasar nau’o’in wasannin lankwasa jiki ta duniya wadda za a yi a shekarar 2027.

Kwamitin shirya gasar wasannin tsalle-tsalle da lankwasa gabobin jiki ko FIG, ya tabbatar da hakan bayan taron sa na birnin Dhaka dake Bangladesh, wanda aka gudanar tsakanin ranaikun 22 zuwa 23 ga watan Nuwamba. FIG ya ce ya karbi sakon birnin na Chengdu na neman karbar bakuncin gasar, wadda za ta gudana a karo na 55, daga hukumar shirya nau’o’in wasannin lankwasa jiki ta kasar Sin.

Bayan karbar sakon, a cewar babban sakataren FIG Nicolas Buompane, ya ce kwamitin FIG ya gudanar da kuri’a domin zabar wurin da za a mikawa ragamar karbar bakuncin wannan gasa, kuma birnin Chengdu na Sin ne ya samu kuri’un amincewa mafiya yawa. An tsara gudanar da wannan gasa ne tsakanin ranar 28 ga watan Satumba zuwa 6 ga watan Oktoban shekarar 2027.

Da wannan sakamako, birnin Chengdu zai zama birnin kasar Sin na 3 da zai karbi bakuncin wannan gasa, bayan birnin Tianjin da ya karba a shekarar 1999, da kuma birnin Nanning da ya karba a shekarar 2014. 

IOC ta amince ta baiwa ‘yan wasa masu zaman kan su damar halartar gasar Olympic ta Paris 2024

Hukumar zartaswar kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa ko IOC, ta amince da baiwa ‘yan wasa masu zaman kan su, wadanda basu da alaka da yaki daga wasu kasashe masu fama da tashe-tashen hankula, damar shiga a dama da su a gasar Olympic da birnin Paris zai karbi bakunci a shekarar 2024 dake tafe, bayan sun cika wasu ka’idoji.

Hukumar ta ce rukunin wadannan ‘yan wasa masu rike da fasfon kasashen Rasha da Belarus, da suka samu gurbin shiga gasannin kasa da kasa daga hukumomin shirya wasanni ko “Ifs”, za su iya shiga a fafata tare da su a gasar ta Paris ta 2024, bayan cika wasu sharudda.

Ya zuwa yanzu, IOC ya ce akwai irin wadannan ‘yan wasa su 11 cikin jimillar ‘yan wasa 4,600, da suka samu gurbin halartar gasar Paris ta 2024, 8 daga cikin su na dauke da fasfon kasar Rasha, yayin da 3 kuma ke dauke da fasfon kasar Belarus. Ana kuma sa ran IOC ko IFs za su mika gayyata ga sauran irin wadannan ‘yan wasa.

A bangaren sa, kwamitin IOC zai shirya tsarin tantancewa ga wannan rukuni na ‘yan wasa, tare da rukunin masu taimaka musu. Kana za a tabbatar da kiyaye ka’idoji da dama, ciki har da tabbatar da cewa ‘yan wasan ba sa goyon bayan yaki, kana ba su da wata alaka da rundunonin sojin Rasha ko Belarus, ko wasu hukumomin tsaron kasashen, kuma ba za su daga tutocin kasashen ba, ko rera taken su, ko sanya launuka, wasu alamu masu nuna goyon bayan Rasha ko Belarus. Har ila yau, dole ne su amince da dukkanin dokokin yaki da shan kwayoyin kara kuzari. Kuma tabbas ba wata kungiya ta ‘yan wasan dake dauke da fasfon kasashen Rasha ko Belarus, da za a bari ta shiga gasar Olympic ta Paris a shekarar 2024 dake tafe.

Wata sanarwa ma da kwamitin IOC ya fitar, ta ce "Za a kare hakkin daidaikun ‘yan wasan motsa jiki da za su fafata a gasar, ciki har da wadanda aka dakatar da hukumomin shirya gasanni na kasashen su, kamar yadda aka saba. Za a ci gaba da kare hakkokin bil adama bisa doka".

A daya bangaren, IOC ya ce zai kara yawan kudaden tallafawa ‘yan wasa masu zaman kan su daga kasar Ukraine zuwa dala miliyan 7.5. Hukumar zartaswar IOC ta ce za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen ingiza nasarorin Olympic, ta fannin taimakawa ‘yan wasan motsa jiki na Ukraine ta dukkanin hanyoyin da suka kamata, ta yadda Ukraine din za ta samu zarafin gabatar da tawaga mai karfi a gasar Olympic ta Paris ta 2024, da gasar lokacin hunturu da za a gudanar a Milano Cortina a shekarar 2026.

Yayin wata ganawa da hukumomin shirya gasannin kasa da kasa suka yi a Talatar makon jiya, hukumomin sun ce za su ja hankalin kwamitin IOC, game da bukatar gaggauta baiwa ‘yan wasa masu zaman kan su, cikakkiyar damar shiga wasannin Olympic yadda ya kamata.

Tuni dai IOC ya jaddada cewa, bai dace a hukunta tarin ‘yan wasan motsa jiki saboda laifin da kasashen su na haihuwa suka aikata ba, inda kwamitin ya ba da misali da yarjejeniyar MDD mai nasaba da tsarin gudanar da gasar Olympic, da sanarwar shugabanni ta New Delhi wadda aka fitar karkashin kungiyar G20, sanarwar da ta tsame ‘yan-ba-ruwan mu daga duk wani takunkumi da shiga yaki ka iya haifarwa, tare da la’akari da bayanan wakilan musamman daga MDD, wadanda suka gabatar da matsayar hukumar kare hakkokin bil adama ta MDD.