Idan ana maganar kamfanonin Sin, ita kanta Burtaniya ma za ta ji radadin
2023-12-20 10:18:41 CMG Hausa
A kwanakin nan ne, kafofin watsa labaru na Burtaniya suka ba da labarin cewa, kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Burtaniya, ya cire abubuwan da kamfanonin kasar Sin suka samar, wai saboda batun "tsaro". Wasu manazarta sun yi nuni da cewa, idan har wannan lamari ya tabbata gaskiya, abin da ake nufi shi ne, bangaren Birtaniyya na cin mutuncin kamfanonin Sin, suna ta yada abin da ake kira wai "barazanar kasar Sin", bayan Amurka, ta kara neman dakile kamfanonin fasahohi na kasar Sin, wanda ke nuna kawance na musamman tsakanin Burtaniya da Amurka. Ban da wannan kuma, kasar Burtaniya za ta gudanar da babban zabe a shekara mai zuwa, kuma jam'iyya mai mulki na fatan samun karin kuri'u ta hanyar kara daukar matakai masu tsauri kan kasar Sin.
Sai dai kuma, Burtaniya ce za ta dandana kudarta: canjin da kamfanin na Burtaniya ke fatan gani zai dauki lokaci mai tsawo kuma yana da tsada, kuma mutanen Burtaniya na iya shan wahala daga farashin makamashi mai yawa na dogon lokaci. Koma bayan babbar tashar samar da wutar lantarki na baya-bayan nan, jan hankali ne kan canjin makamashi, kuma yana da wahala a cimma burin rage fitar da hayaki. Siyasantar da batutuwan kasuwanci da fasaha ta kowane hali, zai iya dakushe kwarin gwiwar manyan kamfanoni na kasa da kasa wajen saka hannun jari a Burtaniya.
Ya kamata mutane masu hankali a Burtaniya su fahimci cewa, kasar Sin abokiyar hulda ce kuma wata dama ce ta samun ci gaba. Hanyar da ta dace da kasashen Sin da Birtaniya su bi wajen yin sulhu, ita ce ta hanyar yin hadin gwiwa a aikace da kuma samun moriyar juna, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kawo moriya ga duniya baki daya. (Ibrahim Yaya)