logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace karuwar yaran da basa zuwa makaranta a arewacin kasar barazana ne babba

2023-12-20 09:25:57 CMG Hausa

A jiya Talata 19 ga wata ne aka kawo karshen babban taron yini biyu  a kan ilimi a jihar Bauchi, inda masana da sauran masu ruwa da tsaki suka tattauna a kan hanyoyin da za a bi a dakile karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar.

A yayin taron, karamin minista a ma’aikatar ilimi ta tarayyar Najeriya Dr Yusuf Sununu ya ce, kowa ya san irin kalubalen da yake addabar sha’anin ilimi a arewacin Najeriya wanda kuma wajibi ne a hada hannu domin maganin su.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Karamin ministan ilimin ya ce, ci gaba da samun karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta tun daga matakin firamare da karamar sakandare a arewacin Najeriya yana haskawa gwamnati cewa, akwai jan aiki a gabanta, wannan ce ta sanya yanzu haka gwamnatin tarayya ke kokarin sake fasalta tsarin koyo da kuma koyarwa a tsarin ilimin kasar.

Ko da yake dai ministan ya ce, yin aiki tare a tsakanin gwamnatocin jihohi da na tarayyar da kuma sauran masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi zai taimaka matuka wajen maganin wasu daga matsalolin da ilimi ke fuskanta a kasar wadanda suka hadar da, “Rashin zuwan yara makaranta, rashin ingantattun malamai, rashin kyakkyawan yanayin koyo da kuma koyarwa, rashin daidaito tsakanin jinsi da kuma wariya, da karancin kayan aiki a makarantun.”

A jawabinsa gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed ya ce, bayan gane mummunan tasirin da matsalolin ilimi ke haifarwa ga ci gaban al`umma, ya sanya gwamnatin jihar ta fara daukar matakan kandagarki da suka hada da, “Kirkirar ma’aikatar lura da ilimi mai zurfi, wannan yunkuri yana da nufin daga matsayin ilimi a dukkan matakai wato tun daga firamare da sakandare da kuma manyan makarantun gaba da sakandire.”

Gwamnan ya ce, yana da yakinin cewa babban taron ilimi da aka kammala zai fito da tsare-tsare da manufofin ingantattu da zai kai ga tsame jihar Bauchi daga jerin jihohin arewa da aka fi samun matsaloli na rashin zuwa makaranta ga yara. (Garba Abdullahi Bagwai)