logo

HAUSA

Dalibin kasar Benin: Ina fatan kawo fasahohin aikin noma na kasar Sin zuwa kasar Benin

2023-12-20 10:08:53 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa, dangantaka tsakanin kasar Sin da kasar Benin tana da zurfi sosai. Tun bayan da aka kulla dangantaka tsakanin kasashen biyu a shekarar 1964, cikin shekaru fiye da 50, a ko da yaushe bangarorin biyu suna abokantaka tare da nuna sahihanci, kuma akwai wani dalibi mai suna Bodjrenou Mahoudjro David daga kasar Benin, wanda ya dade da zama tare da yin karatu a kasar Sin, ya kuma kwashe shekaru da yawa yana neman ilimi. To a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labarin David, wani dalibi daga kasar Benin dake karatu a kasar Sin.