logo

HAUSA

Lokaci ya yi da za a mayar da kayayyakin tagulla na daular Benin gida

2023-12-20 14:30:08 CMG

Daga Lubabatu Lei

Gidan adana kayayyakin tarihi na Burtaniya, wato the British Museum a Turance, ya kasance daya daga cikin gidajen adana kayayyakin tarihi mafi girma kuma mafi dadadden tarihi a duniya, sai dai da yawa daga cikin kayayyaki sama da miliyan 8 da ke gidan, an kwato ko sato su ne daga kasa da kasa a lokacin da Birtaniya ke mulkin mallaka a sassan duniya.

Misali a gidan, akwai kayayyakin tagulla kimanin 900 na daular gargajiya ta Benin wadda a zamanin da ta kasance a kudancin kasar Nijeriya, wadanda Burtaniya ta kwaso su gidan bayan da ta wawushe fadar daular a lokacin da ta kaddamar da yaki kan daular a shekarar 1897. Wadannan kayayyakin tagulla dai sun kasance masu matukar muhimmanci a tarihin fasahar Afirka, haka kuma kayayyakin tarihi masu daraja na al’ummar Nijeriya. Ban da su, a gidan, akwai sassakan marmara na Parthenon na kasar Girika, da dutsen Rosetta na kasar Masar da ma wasu kayayyakin tarihi masu daraja dubu 23 da suka fito daga kasar Sin, wadanda suka shaida mummunan tarihin mulkin mallaka na Burtaniya.

Duk da cewa kasashen Sin da Nijeriya da Girika sun sha bukatar Burtaniya da ta mayar musu da wadannan kayayyakin tarihi, amma kullum Burtaniya ta kan ki bisa dalili na wai “kare lafiyar kayayyakin”.  Amma abin kunya shi ne, a cikin kusan shekaru 30 da suka gabata, gidan adana kayayyakin tarihi na Burtaniya wanda ke daukar kanta a matsayin mai kare lafiyar kayayyakin tarihi, ya sha fuskantar sace-sace a kalla sau shida. Wani rahoton bincike na baya-bayan da gidan ya fitar, ya kuma nuna cewa, daga cikin kayayyakin da gidan bai nuna su ba, akwai kimanin 2000 da suka bace ko aka sace su ko kuma suka lalace.

A game da yanayin tsaro na kayayyakin tarihi da ke gidan, Abba Isa Tijani, babban darektan kwamitin kula da gidajen adana kayayyakin tarihi da kayayyakin tarihi na Nijeriya ya ce, “wasu kasashe da gidajen adana kayayyakin tarihi sun sha bayyana mana cewa, kayayyakin tagulla na daular Benin ba su da tsaro a Nijeriya, amma ga abin da ya faru gare su. Ainihin batun shi ne kayayyakin tarihi ne da aka kwashe, kuma ya kamata a mayar da su gidanjensu ko kasashensu na asali.”

Zamanin mulkin mallaka ya shude, kuma shekaru sama da 120 ke nan da aka kwace kayayyakin tagulla na daular Benin daga Nijeriya, lokaci ya yi da za a mayar da su gida. (Mai Zane: Mustapha Bulama)