logo

HAUSA

Wakilin Sin ya ba da shawarar goyon bayan kokarin kwamitin sulhu na ceton rayuka a Gaza

2023-12-20 10:38:43 CMG

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya jaddada bukatar dukkan mambobin kwamitin sulhu na MDD, da su goyi bayan yunkurin majalisar na ceto rayukan jama'a a Gaza. Wakilin na Sin ya bayyana hakan ne a taron kwamitin sulhu kan halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, ciki har da batun Falasdinu.

Zhang Jun ya ce, kasar Sin tana kira ga dukkan mambobin majalisar, da su dauki matakin da ya dace,tare da goyon bayan majalisar don yanke shawarar da ta dace, tsakanin yaki da zaman lafiya da kuma tsakanin yin rayuwa da mutuwa.

A jiya ne kuma, Zhang Jun ya mikawa babban sakataren MDD Antonio Guterres, takardar amincewar shigar kasar Sin cikin yarjejeniyar yaki da samarwa da safarar makamai ta haramtacciyar hanya. Ya ce, a matsayinta na mambar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma mai kula da al'ummomin kasa da kasa, kasar Sin tana son daukar matakin a matsayin wata dama ta kara karfafa mu'amala da hadin gwiwa da dukkan bangarori a fannin kananan makamai da kuma taimaka wa kasashe masu tasowa inganta kwarewarsu, da gina duniya mai cikakken zaman lafiya da tsaro tare. (Ibrahim)