logo

HAUSA

Yadda Sin ke daukar matakan bunkasa kasuwannin gida da na waje domin raya tattalin arzikinta

2023-12-20 08:12:38 CMG Hausa

Kasar Sin, wacce ke zama kasuwar hada-hadar kayayyaki ta biyu mafi girma a duniya, tana kokarin kara hade kasuwannin cikin gida da na waje.

A kwanakin baya ne, babban ofishin majalisar gudanarwar kasar ya fitar da wata sanarwa, inda ya gabatar da matakai 18 don hanzarta hade wadannan sassa, da nufin karfafa gwiwar kamfanonin cinikayyar waje da hade kasuwannin cikin gida da na waje.

Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sheng Qiuping, ya bayyana a wani taron manema labarai da aka gudanar cewa, hade cinikayyar cikin gida da waje ita ce kiyaye hadin kai da ci gaba da kuma taimakawa kamfanoni tsayawa da kafafunsu

Ya ce, muhimmiyar manufa ta hadewar kasuwancin cikin gida da na waje, ita ce inganta karfin ci gaban masana'antun cikin gida da na waje, ta hanyar inganta tsare-tsare, gina dandamali na bai daya, da inganta ayyuka ta yadda kamfanoni za su dace da sauye-sauyen guda biyu a cikin harkokin kasuwancin cikin gida da na kasa da kasa cikin kwanciyar hankali.

A cewar sanarwar, za a dauki matakan hanzarta daidaita ka'idoji da tsarin kasuwancin cikin gida da na waje da suka hada da ma'auni, gwaji, tantancewa, da kuma sanya ido.

Kazalika, za a yi kokarin inganta hanyoyin da za a hada kasuwannin cikin gida da na waje,kana yanayin cinikayyar cikin gida da na waje, zai inganta tare da daukar matakai da suka hada da kara kare ikon mallakar fasaha, da kyautata tsarin bashi, da inganta kayan aiki. 

A cewar Yao Lei, jami'in hukumar kula da kayyade kasuwanni ta kasar Sin, mai sanya ido kan kasuwannin kasar Sin, ya bayyana cewa, sashen zai himmatu wajen inganta daidaiton ka'idojin cikin gida da na kasa da kasa, tare da karfafa amincewar juna tsakanin kasa da kasa game da tantance daidaito.

Sheng ya kara da cewa, matakan ba wai goyon bayan kamfanonin kasashen waje su fadada kasuwannincinsu a cikin gida ba, ta yadda kayayyaki masu inganci na kasashen waje za su iya shiga cikin dandalin ciniki na intanet na cikin gida, da manyan kantuna, amma za su tallafawa kamfanonin cinikayyar waje don fadada kasuwarsu, ta hanyar ba da cikakkiyar dama ga rawar da sabbin nau'ikan kasuwancin waje da samfura kaya, kasuwancin intanet tsakanin kasashe, da ɗakunan ajiya na ketare ke takawa ga bunkasar tattalin arziki. (Saminu, Ibrahim, Sanusi Chen)