logo

HAUSA

An kama wasu gungun barayi ’yan ta’adda da ke fashi da makami anan birnin Yamai

2023-12-20 13:59:41 CMG Hausa

A birnin Yamai, babbar ma’aikatar ’yan sanda DPJ ta bankado wasu gaggan gungun barayi guda hudu da suka yi karin suna wajen fashi da makami, kisan kai, danfara, sacen kaya, da rike bindiga ba tare da izni ba. A kokarin da hukumomin birnin Yamai suke yi domin kawar da matsalar tsaro a babban birnin kasar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu, Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Ofishin ’yan sanda na PJ dai ya gabatar a ranar jiya Talata, 19 ga watan Disamba na shekarar 2023 da wasu gungun barayi guda hudu da aikinsu shi ne na fashi da makami, kuma dukkan su ’yan kasar Nijar ne, da kuma suka jima suna addabar mazauna birnin Yamai kafin dubunsu ta cika, su shiga hannun ’yan sanda.

Wadannan gungun barayi sun shahara wajen sata cikin dare, da amfani da makamai, da hada kai da wasu domin shiga cikin gidajen mutane, da kuma fashe shaguna.

Ta’asar da suka tafka ta baya bayan nan a cewar shugabannin ’yan sanda na DPJ ta faru ne a cikin daren 30 ga watan Nuwamba zuwa ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2023, inda suka bude wuta kan wasu mutane guda hudu, mambobin iyali guda, daga cikinsu akwai mace guda mai juna biyu, tare da jikkata wasu daga cikinsu da kuma yin awon gaba da jika dari 6 na Sefa. 

Bayan gudanar da bincike, an kama barayin, haka zalika binciken ba zata a cikin gidajen nasu da ya taimaka wajen sanya hannu kan kayayyaki daban daban da suka hada da bindigogi, adduna, sanduna, da kuma sauran kayayyakin da ake amfani da su domin shiga cikin gidaje da kuma fashe shaguna.

Mamane Ada, sashen Hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.