logo

HAUSA

Kamfanin mai na tarayyar Najeriya ya yi alkawarin rinka samar da gangar danyen mai miliyan 2 a kullum daga shekara mai zuwa

2023-12-19 10:19:53 CMG Hausa

An kaddamar da sabbin ’yan hukumar gudanarwar kamfanin mai na tarayyar Najeriya NNPCL, inda suka yi alkawarin cewa daga shekara mai zuwa ta 2024 kamfanin zai rinka samar da gangar danyen mai miliyan biyu a kowacce rana.

A loakcin da yake kaddamar da ’yan hukumar, shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci membobin hukumar da su fara aiki gadan-gadan tare da barazanar rushe su muddin suka gaza tabuga wani abin a zo a gani.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, bangaren mai bangare ne da yake da matukar muhimmancin gaske a wajen gwamnati, a don haka ya zama wajibi sabbin jami’an su zage damtse wajen tabbatar da ganin tasirin bangaren hada-hadar mai na taka rawar da ake hasashen zai taka wajen fitar da Najeriya daga matsalolin tattalin arziki.

Haka kuma shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jaddada bukatar kamfanin man na NNPCL da ya kula sosai wajen lura da hakkokin al’umomin yankin Niger Delta mai arzikin mai ta hanyar kiyayewa da muhallansu, bisa la’akari da yadda harkokin hakar mai ke matukar illata muhalli.

“Wajibi ne mu kalli yankin Niger Delta da muhimmanci ganin irin dimbin arzikin da yankin ke samarwa kasa, akwai bukatar a mutunta yankin tare da kulawar da ta kamata, ta hanyar tabbatar da tsaftaccen ruwan sha, gina makarantu, samar da wuraren lura da lafiya da kuma hanyoyin mota.” 

A jawabinsa, shugaban sabuwar hukumar kamfanin man na tarayyar Najeriya Chief Pius Akinye-lure, ya ce abu na farko da za su fara sanyawa a gaba dai shi ne kara adadin man da ake hakowa a Najeriya sai kuma dakile ayyukan barayin mai da kuma masu fasa bututun mai a yankin na Niger Delta. (Garba Abdullahi Bagwai)