logo

HAUSA

Sin ya yi kira ga al’ummar kasa da kasa su taimakawa Libya gano hanyar ci gaba da ta dace da yanayin kasar

2023-12-19 10:57:19 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya Dai Bing, ya yi kira ga kasashen duniya, da su taimaka wa dukkan bangarorin kasar Libya, wajen gano hanyar samun ci gaba da ta dace da yanayin kasarsu.

Dai Bing ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Libya cewa, tsoma bakin waje da kuma tsara manufofi ta hanyar da ba ta dace ba, ba zai iya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Libya ba, hanya daya tilo da ya kamata a bi ita ce, mutunta ikon mulki da shugabancin kasar Libya da taimakawa dukkanin bangarorin dake kasar Libya wajen binciko hanyar ci gaban da ta dace da yanayin kasarsu. Kasar Sin tana goyon bayan tawagar MDD dake kasar Libya wajen ci gaba da inganta tattaunawa da tuntubar juna, da daidaita matsalolin da suka dace na dukkannin bangarori, da kuma taka rawa mai ma’ana.

Dai Bing ya kara da cewa, bangaren Sin ya lura da cewa, kara yawan man fetur da ake hakowa a kasar Libya, ya sa tattalin arzikin kasar samun ci gaba a kai a kai. Kuma an yi hasashe cewa, saurin ci gaban tattalin arzikin kasar a bana zai kai kashi 14%, wanda ya cancanci yabo sosai. A sa’i daya kuma, bala’in ambaliyar ruwa da ya faru a kasar, ya haifar da mummunan matsalar jin kai, a hannu guda kuma, ayyukan sake farfadowa bayan bala'u a yankuna da dama na da wahala. Kasar Sin ta yi maraba da kokarin da mahukuntan kasar Libya da dukkannin bangarori suka yi, tare da yin kira ga kasashen duniya da su kara kai agajin jin kai kasar. (Safiyah Ma)