logo

HAUSA

Shugaban Masar mai ci ya lashe zaben shugabancin kasar da 89.6%

2023-12-19 09:42:41 CMG Hausa

 

Hukumar zaben Masar (NEA) ta sanar a jiya Litinin cewa, shugaban kasar mai ci Abdel-Fattah al-Sisi, ya lashe zaben shugabancin kasar na shekarar 2024 da aka gudanar da kashi 89.6 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

A wani taron manema labarai da ta gudanar a Alkahira, babban birnin kasar, hukumar ta ce, adadin wadanda suka kada kuri'a, ya kai kashi 66.8 cikin 100 na mutane miliyan 67 da suka cancanci kada kuri'a.

An gudanar da zaben shugabancin Masar ne, tsakanin ranakun 10 zuwa 12 ga watan Disamba, yayin da al'ummar Masar dake zaune a kasashe daban daban 121 a ketare, suka kada nasu kuri'un, tsakanin ranakun 1 zuwa 3 ga watan Disamba.

'Yan takara hudu ne dai suka fafata a zaben shugabancin kasar, wadanda suka hada da al-Sisi, da Farid Zahran na jam’iyyar Social Democratic, da Abdel-Sanad Yamama na jam'iyyar Al-Wafd, da Hazem Omar na jam'iyyar People's Republican. (Ibrahim)