logo

HAUSA

Sin ta sami gaggaumin ci gaba wajen gina tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje

2023-12-19 15:44:57 CMG Hausa

 

Masu kallonmu, barka da war haka. A watan Disamban shekarar 1978, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje. Cikin shekaru 45 da suka gataba, kasar Sin ta dauki matakai yadda ya kamata domin inganta yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje, matakan da suka raya tattalin arzikin kasar, da ba da gudummawar gina tsarin tattalin arziki mai salon bude kofa ga kasashen waje. A halin yanzu, kasar Sin ta kafa zumunci mai zurfi da kasashen duniya wanda da ba a taba ganin irinsa ba a tarihin kasar.