logo

HAUSA

Guinea: Adadin wadanda suka mutu a gobarar da ta tashi a wata ma'ajiyar ajiyar kaya ya kawu zuwa 13

2023-12-19 09:50:49 CMG Hausa

Wani jami’in kare fararen hula a kasar Guinea, ya bayyana cewa, a kalla mutane 13 ne suka mutu kana wasu 170 suka jikkata, bayan fashewar wani abu da ta haddasa gobara a babban ma'ajiyar man fetur dake kasar Guinea a ranar Litinin.

Darektan gudanarwa ta fuskar fasaha a hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, Jean Traore ya shaidawa taron da ministan harkokin waje da jakadu suka halarta cewa, hukumar ta kidaya gawarwakin mutane 13, baya ga wasu 170 da suka samu munanan raunuka a lamarin da ya faru a babban birnin kasar Conakry.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce, ba a san abin da ya haddasa gobarar ba, kuma za a gudanar da bincike don gano musabbabinta, da ma wanda ke da hannu a lamarin.

Ana iya ganin wuta da bakin hayaki na ci daga nisan mil guda, yayin da jami’an kashe gobara suka garzaya zuwa wurin, kana wasu manyan motocin dakon mai suna ficewa daga ma’ajiyar tare da rakiyar sojoji da ‘yan sanda.

An shawarci ma’aikata, in ban da jami’an tsaro da ma’aikatan lafiya, da su kasance a gidajensu. An kuma rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu da ma galibin gidajen mai.(Ibrahim)