logo

HAUSA

Yadda ake gudanar da ayyukan ceto bayan aukuwar girgizar kasa a lardin Gansu na kasar Sin

2023-12-19 14:33:20 CMG Hausa

Yadda ake gudanar da ayyukan ceto bayan aukuwar girgizar kasa a lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin. Da misalin da karfe 12 saura minti 1 na daren jiya ne, girgizar kasa mai karfin maki 6.2 ta afkawa gundumar Jishishan na lardin Gansu. Ya zuwa yanzu, girgizar kasar ta yi sanadin mutuwar mutane 100 a Gansu, baya ga wasu 11 da suka mutu a lardin Qinghai da ke makwabtaka.