logo

HAUSA

Ko yin barci fiye da kima da tsoffi suka yi a rana yana alamta karuwar barazanar kamuwa da Alzheimer's disease?

2023-12-19 11:03:18 CMG Hausa

 

Wani nazarin da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna cewa, karuwar tsawon lokacin barci da tsoffi suka dauka a rana, yana da nasaba da karuwar hadarin kamuwa da cutar Alzheimer's.

Mece ce cutar Alzheimer's? Ita ce wani nau’in ciwon karancin basira da dake farawa daga matsalar mantuwa, daga bisani ya shafi tunanin mutane da kwarewar magana har ma da gudanar da harkokin yau da kullum. Kafar CNN ta Amurka ta ruwaito rahoton nazarin a kwanan baya cewa, a cikin tsoffi kimanin dubu 1 da dari 4 Amurkawa dake cikin nazarin, gwarwadon wadanda tsawon lokacin barci bai wuce awa daya a rana ba, wadanda su kan dauki fiye da awa daya suna barci a rana sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar Alzheimer's har kashi 40 cikin kashi 100. Kana kuma, gwargadon wadanda ba safai su kan yi gajeren barci da rana ba, wadanda su kan yi gajeren barci a kalla sau daya a ko wace rana sun fi fuskantar hadarin kamuwa da cutar Alzheimer's har kashi 40 cikin kashi 100.

Masu nazarin daga reshen jami’ar California ta Amurka a San Francisco sun gayyaci wadannan tsoffafi daga unguwanni fiye da 30 a birnin Chicago da su shiga nazarinsu daga watan Satumban shekarar 1997 zuwa watan Afrilun shekarar 2005. A lokacin da aka fara nazarin, shekarun wadannan tsoffi na tsakanin 74 zuwa 88 a duniya. Dukkansu ba su kamu da cutar Alzheimer's ba.

Masu nazarin ba su tabbatar da cewa, yin barci da yawa a rana, dalili ne dake sanya kamuwa da cutar ta Alzheimer's ba. Suna ganin cewa, watakila idan wasu sun yi barci da yawa da rana, to, ga alama za su yi saurin tsufa ko kuma su samu saurin lalacewar kwarewar fahimta. Don haka kamata ya yi a lura sosai da tsoffafi dangane da tsawon lokacin barci da su kan dauka da rana. A sanar da likitoci kan lokaci idan tsoffafi sun yi barci da yawa da rana. (Tasallah Yuan)