Bangarorin dake rikici da juna a Sudan na ci gaba da musayar wuta a yankin tsakiyar kasar
2023-12-18 11:29:45 CMG Hausa
Dakarun tsaron Sudan da rundunar kai daukin gaggawa (RSF) sun ci gaba da yin musayar wuta a yankin Umm Alila dake gabashin Wad Madani, babban birnin jihar Gezira dake tsakiyar kasar a jiya Lahadi.
Rundunar Sojin Sudan ta yi ikirarin dakile wani harin da dakarun kai daukin gaggawa suka kai a wannan rana, wanda ya yi sanadiyar asarar daruruwan rayuka a daya bangaren. Amma RSF ta sanar da cewa, ta mamaye wasu yankunan gabashin jihar Gezira.
Haka kuma, a wannan rana an sha igwa a yankunan birnin Wad Madani, kuma mahukuntan yankin sun yi kira ga jama’a da su zauna a cikin gidajensu.
Tun bayan barkewar rikici a Sudan a watan Afrilu na bana, ba a tayar da kwanciyar hankali a jihar Gezira ba, sakamakon haka, ’yan gudun hijira kusan dubu 500 sun shiga jihar sun kuma zauna a wurin. Yayin da fada ya bazu zuwa birnin Wad Madani, fararen hula da dama sun tsere daga yankin.
Kwamitin likitoci na Sudan ta yi gargadi a jiya Lahadi cewa, jihar Gezira tana gab da fuskantar bala’in jin kai, sakamakon haka, mai yiyuwa ne babu sauran zabi, sai dai dubban daruruwan ’yan gudun hijira dake zaune a wurin, dole ne su ci gaba da gudu zuwa sauran yankuna.
A wannan rana hukumar lafiya ta duniya da ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, sun yi kira ga bangarorin biyu dake rikici da juna a Sudan, da su tsagaita bude wuta a birnin Wad Madani, domin magance kara tsanantar yanayin jin kai da ake ciki a birnin. (Safiyah Ma)