logo

HAUSA

Muhimmancin manufofin Sin wajen ingiza ci gaban duniya

2023-12-18 21:59:48 CMG Hausa

A bana ake bikin cika shekaru 45 da kaddamar da manufar kasar Sin ta aiwatar da gyare gyare da bude kofa. Gyare gyare da bude kofa ba kawai sun haifar da babban sauyi ne a kasar Sin ba, har ma matakin ya haifar da hadin gwiwar cimma moriya tare da sauran sassan duniya.

A cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta matsa daga matakin bude kofa mai nasaba da fitar da hajoji da matakan bunkasar hakan, zuwa bude kofa bisa dokoki, da ka’idoji, da jagoranci, da tabbatar da inganci, wanda hakan ke nuna yadda manufar "Bude kofa” ta zama muhimmin ginshiki na bunkasa ci gaban kasar.

Budadden tsarin tattalin arzikin kasar Sin, ya kuma ba da gudummawa ga bunkasar tattalin arziki a matakai na zahiri. Har kullum Sin na kasancewa muhimmin jigo na ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda muhimmin ginshiki ne musamman a lokacin da yanayin farfadowar tattalin arzikin duniya ba shi da karfi sosai. Ga manyan kamfanonin duniya, suna cin gajiya daga bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, tare da samun karin damammakin ci gaba a kasar Sin.

Salon Sin na bude kofa, daya ne daga dalilan bunkasar tattalin arziki maras gurbata muhalli da na dijital. A shekarar 2022, sashen raya tattalin arzikin Sin na dijital ya kai kaso 41.5 bisa dari na GDPn kasar, wanda ya kai matsayi na 2 a duniya.

Ga misali, a nahiyar Afirka, tsarin amfani da fasahar sadarwa ta dijital wajen aikewa da sakwanni na Sin, ya taimakawa ‘yan Najeriya wajen yin sayayya ta yanar gizo cikin sauki. Tsarin fasahohin Sin na bunkasa ci gaba na dijital, yana amfanar jama’a dake sassan duniya daban daban, tare da ingiza sabon kuzari ga bunkasar tattalin arzikin duniya.

Bugu da kari, kwazon Sin game da bude kofa, da himmarta wajen gina budadden tattalin arzikin duniya, ya samar da sabuwar mahanga ga tsarin jagorancin duniya. Har kullum Sin na nacewa salon tattaunawa mai zurfi, da gudummawar bai daya da cin gajiya tare, tana kuma maraba da dukkanin sassan duniya da su ci gajiya daga damammakin da take samarwa.  (Saminu Alhassan)