logo

HAUSA

’Yan ta’adda sun hallaka wasu manoma hudu a yayin da suke aikin girbin hatsi a jihar Katsina

2023-12-18 09:16:28 CMG Hausa

Wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne sun hallaka wasu manoma hudu tare da yin garkuwa da wasu mutum 8 a kauyen Nahuta dake yankin karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.

’Yan ta’addan sun afkawa manoman ne da tsakar ranar Asabar 16 ga wata a lokacin da suke gudanar da aikin girbin hatsi.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar ta Katsina ASP Abubakar Sadik Aliyu ne ya tabbatar da faruwar al’amarin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar ’yan sanda ta birnin Katsina.

Ya ce, ’yan ta’addan dai sun gudanar da wannan hari ne da bindigogi kirar AK47, inda nan take suka fara bude wuta ga mutanen da suke gudanar da aiki a cikin wata gona.

Kamar yadda kakakin rundunar ’yan sandan ya bayyana, mutum guda ne ya samu ya tsira da ransa bayan shi ma ya samu raunika daga harbin bindiga.

Sai dai a ganawar musamman da na yi da kakakin ’yan sandan na jihar Katsina da misalin karfe 9 na daren Lahadi agogon Najeriya ya shaida mun cewa, 

“Da samun wannan rahoto, mai girma kwamashinan ’yan sanda reshen jihar Katsina CP Aliyu Abubakar Musa ya tura dakarun shi wannan wuri, inda ya hore su da su tabbatar da ganin cewa sun kubuto da wadanan mutane cikin koshin lafiya, kuma alhamdulillahi yanzu da nake magana da kai haka cikin mutane 8 mutane biyar suna nan a yanzu an samo su suna nan tare da iyalansu cikin koshin lafiya, kuma rundunar tana nan tana iya bakin kokarinta don ganin cewa ta samo sauran da suke rike a hannun wadannan ’yan ta’adda, baya ga haka mai girma kwamashinan ’yan sanda ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai da ’yan uwa da abokan wadanda wannan iftila’i ya ritsa da su.”

Tuni dai rundunar ’yan sanda ta jihar Katsina ta sabunta tsare-tsaren sha’anin tsaro a wannan yankin don ganin an dakile sake faruwar wani abu makamancin haka a nan gaba. (Garba Abdullahi Bagwai)