logo

HAUSA

Ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta kori jami’an diflomasiyyar Chadi guda 4

2023-12-18 11:15:20 CMG Hausa

Jiya Lahadi, ma’aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta ayyana jami’an diflomasiyyar Chadi guda 4 dake kasar Sudan, a matsayin wadanda ba a maraba da zuwansu kasar Sudan, ta kuma bukace su da su fice daga kasar cikin sa’o’i guda 72.

A ranar 16 ga wata ne dai, gwamnatin kasar Chadi ta kori jami’an diflomasiyyar Sudan guda 4 daga kasarta, ta kuma neme su da su fice daga kasar Chadi cikin sa’o’i 72. Kana, cikin wata sanarwar da gwamnatin kasar Chadi ta fidda, ta nuna cewa, ta dauki wannan mataki domin mai da martani ga kasar Sudan game da “kalamai na rashin hankali” da shugaban rundunar soja, kana mamban a majalisar mulkin kasar Sudan Yasir al-Atta ya yi, kuma, kasar Chadi tana zarginsa da tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.

A karshen watan Nuwamba na bana ne, Yasir al-Atta ya zargi gwamnatin kasar Chadi da baiwa Hadaddiyar Daular Larabawa damar jigilar makamai da alburusai ga rundunar kai daukin gaggawa (RSF) ta jiragen saman kasar Chadi. Zargin da ya haddasa sabani a tsakanin kasashen Sudan da Chadi da UAE. A farkon watan Disamba, kasashen Sudan da hadaddiyar daular Larabawa suka kori jami’an diflomasiyyar juna daga kasashensu. A kwanakin baya ne, gwamnatin Chadi ta kira jakadan Sudan dake kasar Chadi, inda ta bukaci Sudan da ta nemi gafarar kalaman Atta. Amma daga baya mukaddashin ministan harkokin wajen Sudan Ali Sadiq ya ce, Sudan ba za ta nemi afuwa ba. (Maryam Yang)