logo

HAUSA

A kalla mutane 99 sun rasa rayukansu sakamakon hari ta sama da sojojin Isra’ila suka kai a yankin Gaza

2023-12-18 11:28:52 CMG Hausa

Jiya da dare, sojojin Isra’ila sun hai hare-hare ta sama kan Jabalia dake arewacin yankin Gaza. Kakakin ma’aikatar kiwon lafiyar yankin Gaza ya bayyana cewa, hare-hare ta sama da sojojin Isra’ila suka kai kan sansanin ’yan gudun hijira na Jabalia a jiya, sun yi sanadiyar mutuwar Falasdinawa 90.

Rahotanni sun ce, Isra'ila ta kuma kai hare-hare ta sama kan sansanin ’yan gudun hijira na Nusayrat da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe a kalla mutane takwas tare da jikkata wasu da dama.

A cewar gidan talabijin na Al Jazeera, mutum daya ya mutu sannan wasu a kalla uku sun jikkata sakamakon harin da Isra'ila ta kai kan asibitin Nasser na birnin Khan Younis.

Har yanzu Isra'ila ba ta ce kome ba kan wadannan rahotanni. (Maryam Yang)