logo

HAUSA

Wakilin Sin na musamman ya halarci bikin rantsar da shugaban Madagascar

2023-12-18 10:13:17 CMG Hausa

Bisa gayyatar da shugaban kasar Madagascar Andry Nirina Rajoelina ya yi masa, manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, Hu Chunhua, ya halarci bikin rantsar da shugaba Rajoelina da aka yi ranar Asabar, ya kuma gana da shi a jiya Lahadi.

Hu ya mikawa Rajoelina sakon gaisuwa da fatan alheri daga Xi. Ya ce kasar Sin tana mai da hankali matuka kan raya dangantakar dake tsakaninta da Madagascar, kuma tana son yin aiki tare da Madagascar, don zurfafa mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu a fannoni daban daban, da ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan muhimman batutuwan dake shafar moriyarsu, da ciyar da hadin gwiwarsu zuwa wani sabon mataki.

A nasa bangare kuwa, shugaba Rajoelina ya gode wa shugaban kasar Sin bisa aiko da manzo na musamman don halartar bikin rantsar da shi, inda ya bukaci Hu da ya mika sakon gaisuwa da fatan alheri ga Xi.

Ya bayyana cewa, Madagascar tana mutunta dadadden zumuncin dake tsakaninta da Sin, kuma a shirye take ta kara yin hadin gwiwa da kasar Sin a muhimman fannoni kamar aikin gona, da masana'antu, da makamashi da albarkatun jama’a, don ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani babban matsayi. (Ibrahim)