Aljeriya ta amince da shiga yarjejeniyar AfCFTA
2023-12-17 16:37:35 CMG Hausa
Ministan ma’aikatar cinikayya da bunkasa fitar da hajoji na kasar Aljeriya Tayeb Zitouni, ya ce kasar sa ta amince da shiga yarjejeniyar ciniki maras shinge ta nahiyar Afirka ko AfCFTA, domin kasancewa daya daga kasashen da za su shiga a dama da su wajen aiwatar da ita.
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki, wanda ya gudana a birnin Algiers, ciki har da manyan masana tattalin arziki, da jami’ai daga sassan nahiyar Afirka, da babban sakataren yarjejeniyar Wamkele Mene.
Cikin jawabin sa yayin bayyana matsayar Aljeriya, minista Zitouni, ya bayyana muhimmancin shigar kasarsa wannan yarjejeniya a shiyyar da take, yana mai cewa, hakan zai samar da zarafi na musaya tsakanin sassan raya tattalin arzikin Aljeriya da sauran takwarorin kasar mambobin yarjejeniyar ta AfCFTA, kana hakan zai bunkasa burin Aljeriya na fitar da karin hajojin ta da ba na albarkatun man fetur ba, da goyon bayan kasar a fannin fadada sassan cinikayyar kasashen Afirka karkashin yarjejeniyar. (Saminu Alhassan)