logo

HAUSA

Majalissar dattawan Najeriya ta bukaci samun kaso 10 a kasafin da ake warewa bangaren noma

2023-12-17 15:51:00 CGTN HAUSA

 

Yayin da ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar Najeriya ke ci gaba da kare kasafin kudinsu na 2024, majalissar dattawan kasar ta bukaci bangaren zartarwa da ya tabbatar da samar da kaso10 ga bangaren noma a kasafin kudin kowace shekara domin habaka noman abinci a kasa.

Shugaban kwamitin harkokin ci gaban noma na majalissar Sanata Salihu Mustafa ne ya bukaci hakan lokacin da yake jagorantar zaman kare kasafin kudin shekara ta 2024 na ma’aikatar gona da samar da abinci .

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.