logo

HAUSA

Yarjejeniyar zuba jari tsakanin bangarori daban daban da Sin ta gabatar ta samu goyon baya daga dukkanin fannoni

2023-12-17 16:25:42 CMG Hausa

Kwanan baya, an kira taron babbar hukumar gudanarwa ta kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, inda mambobin kungiyar kusan 120, ciki har da kasar Sin suka sanar da cewa, an kammala sake duba takardar “yarjejeniyar saukaka zuba jari domin ingiza ci gaba” bisa ma’aunin doka, kuma sun yi kira ga daukacin mambobin kungiyar da su gaggauta daukar matakai da suka wajaba, na shigar da yarjejeniyar cikin tsarin dokokin kungiyar cinikayyar ta duniya.

Yayin taron da aka kira, zaunannen wakilin kasar Sin dake WTO Li Chenggang ya bayyana cewa, yarjejeniyar ta saukaka zuba jari, domin ingiza ci gaba, kana tana nacewa muradun samun ci gaba, lamarin da ya nuna buri daya, wato ingiza ci gaba ta hanyar zuba jari na mambobin kungiyar.

Ana iya cewa, yarjejeniyar muhimmin sakamako ne da aka samu bisa ajandar bunkasuwa ta WTO, wadda za ta tabbatar da ci gaban kungiyar yadda ya kamata.

Ban da haka, mambobin kungiyar sama da 30, wadanda suka fi fama da talauci kamar Cambodiya, da Laos, da Liberiya, sun gabatar da jawabai yayin taron, inda suka yi bayani kan rawar gani da yarjejeniyar za ta taka, a bangarorin kyautata muhallin zuba jari, da samun jari mai inganci, da habaka ci gaban tattalin arziki, da kuma tabbatar da ajandar samun dauwamammen ci gaba ta MDD nan da shekarar 2030.

Batun saukaka zuba jari, babban batu ne na farko da kasar Sin ta gabatar wa kungiyar WTO, tare da wasu kasashe masu tasowa, kuma yarjejeniyar za ta kasance ta farko a fadin duniya, ta fannin zuba jari tsakanin bangarori daban daban. (Jamila)