logo

HAUSA

Jihar California da kasar Sin sun nuna kyakkyawan misali na tasirin kyautata yanayi domin cimma gajiyar kiwon lafiya

2023-12-17 20:29:45 CMG Hausa

Wani rahoto da cibiyar CCCI, ta hadin gwiwar kula da yanayi ta jihar California ta kasar Amurka da kasar Sin ta wallafa a ranar Alhamis, ya ce shawo kan kalubalen gurbatar iska, da fitar da iska mai dumama yanayi, na iya haifar da moriya ta fuskar kiwon lafiya, kuma jihar California, da hadin gwiwar kasar Sin, sun samar da wani kyakkyawan misali a wannan fanni, wanda duniya baki daya za ta iya koyi da shi.

Rahoton ya ce jihar California ta nuna a fili, yadda za a iya amfani da matakin kiwon lafiyar al’umma a matsayin makin auna nasarorin da aka cimma, a fannin ingancin yanayi da tsaftar iska. A daya bangaren kuma, kasar Sin ta yi fice wajen samar da nau’o’in mizani, da managartan manufofin awon ingancin iska.

Har ila yau, rahoton ya ce darussa, da kwarewar kasashen 2, sun samar da mahanga ga sauran yankunan duniya a fannin dabaru mafiya dacewa da za a iya kwaikwaya.

Bugu da kari, a cewar rahoton na CCCI, California da Sin na da buri guda, a fannin samar da iska mai inganci, da yanayi mai kyau, suna kuma aiwatar da manufofi daban daban na cimma wannan buri nasu, tare da gabatarwa duniya yadda manufofin kare yanayi ka iya haifar da gajiya ta fannin kiwon lafiya.

CCCI cibiya ce mai kunshe da gungun kwararru, karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar California Jerry Brown, wadda ke maida hankali ga ingiza aiwatar da matakan kyautata yanayi, ta hanyar bincike da bayar da horo, da tattaunawa tsakanin masanan California da na kasar Sin. (Saminu Alhassan)