logo

HAUSA

Najeriya: Hauhawar farashin kaya ya karu zuwa kaso 28.2 bisa dari a watan Nuwamba

2023-12-17 16:25:51 CMG Hausa

Hukumar kididdiga ta tarayyar Najeriya NBS, ta ce alkaluman hauhawar farashin kayayyaki a kasar sun daga zuwa kaso 28.2 bisa dari a watan Nuwamban da ya gabata.

NBS ta ce alkaluman awon sauyin tsadar kayayyaki da na hidimomi ko CPI, wanda da shi ne ake auna mizanin hauhawar farashi, ya daga da kaso kusan 6.73 bisa dari, sabanin na watan Nuwambar 2022, wanda ya tsaya kan kaso 21.47 bisa dari.

Hukumar kididdigar ta ta’allaka karin da aka samu ya zuwa watan na Nuwamban bana, da na watannin shekarar, da karuwar hajoji da hidimomin da ake hada-hadar su a matakai daban daban. Kaza lika, karuwar ta fi yawa a fannin kayan abinci, da kayan sha wadanda ba na barasa ba. Sai kuma gidaje, da ruwan sha, da lantarki, da iskar gas, da sauran nau’o’in makamashi, da tufafi da takalma da sufuri.

Bugu da kari, NBS ta ce sauran kayayyakin da farashin su ya yi tashin gauron zabi sun hada da na kawata gida kamar kujeru da gadaje, da abubuwan amfani a gidaje da na gyare-gyare, da na amfani da makarantu, da fannin lafiya, da sauran kayayyakin bukata, da fannin ba da hidima. Sauran sun hada da na amfani a gidajen cin abinci da otal-otal, da nau’o’in barasa, da taba sigari, da goro, da kayan motsa jiki da na raya al’adu, da na fannin sadarwa.  (Saminu Alhassan)