logo

HAUSA

Mutane 61 sun mutu sakamakon nutsewar jirgin ruwa a tekun dake arewacin Libiya

2023-12-17 16:20:15 CGTN HAUSA

 

Hukumar lura da masu kaura ta kasa da kasa, ta ce wani jirgin ruwa dauke da ‘yan ci rani, ya nutse a tekun dake arewacin Libiya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane 61.

Hukumar ta bayyana hakan ne a jiya Asabar, a kan shafin ta na yanar gizo, inda ta ce cikin wadanda suka rasu har da mata da yara. Wadanda suka tsira da ransu yayin hadarin sun ce jirgi na dauke ne da fasinjoji kimanin 86, ya kuma tashi daga birnin Zuwar dake arewacin kasar ta Libiya da nufin tsallaka teku.

Tun daga shekarar 2011, Libiya ke fama da rikice-rikicen siyasance, inda ‘yan ci rani ta barauniyar hanya suka mayar da kasar wurin yada-zango a kan hanyar su ta tsallakawa nahiyar Turai ta tekun Bahar Rum.

Kididdiga daga hukumar lura da bakin haure ta nuna cewa, tun daga farkon wannan shekara kawo yanzu, an tuso keyar ‘yan cin rani ta barauniyar hanya har dubu 15 zuwa Libiya. (Amina Xu)