logo

HAUSA

ECOWAS ta dakatar da wakilcin Nijar a hukumance

2023-12-16 15:42:52 CMG Hausa

 

Kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS, ta dakatar da jamhuriyar Nijar daga dukkanin hukumomin yankin, har sai kasar ta koma ga aiki da kundin tsarin mulki. Kasashe mambobin ECOWAS din su 15 ne suka cimma wannan matsaya a hukumance.

Wata sanarwar da hukumar gudanarwar kungiyar ta aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Jumma’a, ta ce an yanke shawarar dakatar da Nijar din ne sakamakon matsayar da majalisar shugabannin kasashe da gwamnatocin yankin suka cimma, yayin taron gama gari karo na 64 da suka kammala a ranar 10 ga watan nan, a birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Sanarwar ta ce, har yanzu shugaba Mohammed Bazoum, wanda sojoji suka hambarar daga mulki a karshen watan Yuli, shi ne halastaccen zababben shugaban mulkin dimokaradiyya a Nijar.

Kafin hakan, cikin sanarwar kammala taron gama gari karo na 64, shugabannin kasashe mambobin kungiyar sun jaddada wajibcin sakin shugaba Bazoum, tare da sukar matakin ci gaba da tsare iyalinsa, da makarrabansa, da ma gazawar rundunar tsaron kasar ko CNSP, ta komawa bin kundin tsarin mulkin kasar.  (Saminu Alhassan)