logo

HAUSA

Ya kamata a aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD kan hana bazuwar makamai kanana

2023-12-16 16:25:25 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun, ya yi jawabi a gun taron kwamitin sulhu na MDD kan batun barazanar da kananan makamai ke haifarwa ga zaman lafiya a duniya, yana mai cewa, ya kamata a duba, tare da aiwatar da kudurin kwamitin sulhun kan hana bazuwar kananan makamai.

Zhang Jun ya bayyana cewa, domin daidaita matsalar kananan makamai, Sin ta ba da shawarwari hudu, wato kawar da tushen yaduwar makamai, da sa kaimi ga kasashen da abin ya shafa da su sauke nauyin dake wuyansu, su duba yiwuwar aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD kan dakile bazuwar makamai, da kuma baiwa MDD damar taka rawar ganinta a wannan fanni.

Zhang Jun ya ce, Sin za ta yi hadin gwiwar kiyaye bazuwar kananan makamai, da yin kokarin aiwatar da kiran kawo karshen yake-yake, da rikici a nahiyar Afirka. (Zainab)