Sabon matsayin dangantakar kasashen Sin da Vietnam shi ne abin da jama'a ke so
2023-12-15 10:59:01 CMG Hausa
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kasar Xi Jinping, ya kai ziyarar aiki kasar Vietnam daga ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan. Sakamako mafi muhimmanci da aka samu a yayin ziyarar shi ne, bangarorin kasashen biyu sun sanar da cewa, za a gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya dake da ma’ana bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, wanda hakan ke nufin an shiga sabon mataki na ci gaban dangantaka tsakanin jam’iyyun siyasa biyu, da kuma kasashen biyu wato Sin da Vietnam.
Al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tsakanin kasashen Sin da Vietnam, ita ce sakamako da kyakkyawar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen biyu ta haifar a cikin shekaru 15 da suka gabata, wanda ya nuna cewa, bangarorin biyu sun kara amincewar juna a kan siyasa, sun kara inganta hadin gwiwar tsaro, sun kara zurfafa hadin gwiwa mai amfani, da kara inganta tushen ra'ayoyin al’ummun kasashen biyu, sun kara yin mu’ammala da hadin kan bangarori daban-daban, da kuma kara warware bambance-bambance.
Masharhanta sun bayyana cewa, wannan sabon matsayin da aka shiga, shi ne gado da kuma fadadar dangantakar gargajiya tsakanin kasashen biyu, da kuma jam’iyyun siyasa na kasashen biyu. A sa’i daya kuma, zabi ne yayin da manyan jami’an kasashen Sin da Vietnam suke kara mu’ammala da juna, da kuma samun sakamakon hadin gwiwa mai inganci a cikin ’yan shekarun nan, wanda ya cimma moriyar al’ummun kasashen biyu, da kuma burukansu. Tasirinsa ya zarce tasirin da dagantakar bangarori biyu ta kawo, domin ya kawo alherai ga zaman lafiya da ci gaban yankunan.
Kamar yadda Sinawa kan ce, dangogi suna yiwa juna fatan alheri, haka ma makwabta. Taimakon makwafta taimakon kai ne. Kasashen Sin da Vietnam sun gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya dake da ma’ana bisa manyan tsare-tsare, kana zai zama sabon wurin bude ci gaban dangantakar kasashen biyu. Hakan ba ma kawai ya kyautata rayuwar al’ummun kasashen biyu ba, har ma ya ingiza karfi mai inganci ga yankin Asiya da Pasifik da kuma dukkanin duniya. (Safiyah Ma)