logo

HAUSA

UNESCO da Huawei sun hada hannu don mika kayan aikin ICT ga makarantun Habasha

2023-12-15 10:51:43 CMG Hausa

Hukumar kula da ilimi da kimiya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) da kamfanin sadarwa na Huawei na kasar Sin, sun hada hannu wajen kai kayayyakin fasahar sadarwa na zamani (ICT) ga ma'aikatar ilmi ta kasar Habasha.

An ba da tallafin ne a matsayin wani bangare na hadin gwiwar UNESCO da Huawei a karkashin shirin ba da tallafin kayayyakin fasahar zamani ga makarantu (TeOSS), a cewar Huawei a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Alhamis.

A yayin bikin mika kayayyakin, ministan ilimi Ayelech Eshete ta yabawa UNESCO da Huawei bisa jajircewarsu wajen raya harkokin ilimi da kuma yadda suke bayyana ra’ayoyinsu na samar wa al’umma damar samun moriyar fasahar zamani.

Manufar shirin na TeOSS, shi ne samar da tsarin karatu ta hanyar fasahar zamani mai jure rikici ta yadda za a samu damar ci gaba da yin karatu a makarantu ko a gida a kowane irin hali na kwanciyar hankali ko na rikici, a cewar sanarwar. (Yahaya)