logo

HAUSA

Janyewar sojojin Faransa daga Nijar na ci gaba da gudana kamar yadda aka tsaida

2023-12-15 09:03:57 CMG Hausa

A jamhuriyar Nijar, sojojin Faransa na ci gaba da aikin janyewa daga kasar, bayan dangantaka da ke tsakanin kasashe biyu ta lalace tun bayan rikicin siyasa da ya biyo bayan ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, kamar yadda hukumomin rikon kwarya suka bayyana a ranar 13 ga watan Disamban shekarar 2023.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A cikin gidan talabijin din kasar Nijar “Tele-Sahel” aka rawaito cewa, wasu sojojin Faransa 1346 tare da kuma kashi 80 cikin 100 na kayayyaki aka kwashe daga kasar Nijar. Ya zuwa wannan rana, a cewar sanarwar, sojojin Faransa 157 gaba daya suka rage a wannan kasa da ke yammacin Afrika, daga cikinsu akwai masu kula da kayayyaki su 75.

Tun dai bayan juyin mulkin da ya kifar da shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2023, sabbin hukumomin Nijar a karkashin jagorancin shugban kasa, kuma shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, Birgadiye janar Abdourahamne Tiani suka bukaci janyewar sojojin Faransa 1500 da ke sansanonin soja dake yankin Tillabery da kuma birnin Yamai. Haka kuma hukumomin soja a Nijar sun yi allawadai tare da soke yarjejeniyar soja tare da hukumomin Paris.

Duk da tattaunawa mai sarkakiya da kasar Nijar, a karshe dai Faransa ta amince da ta janye dakarunta daga kasar, kuma shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya tabbatar da cewa za’a kammala janye sojojin daga kasar Nijar nan da karshen shekarar 2023.

Sojojin Faransa dai sun kwashe shekaru fiye da goma a Nijar da sunan yaki da ta’addanci, sai dai kasancewar wadannan sojoji hakan bai taimaka ba wajen kawo karshen ta’addancin a Nijar da ma sauran kasashen yankin Sahel.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar. (Maman Ada)