logo

HAUSA

Sin: Ya Kamata Kasashen Duniya Su Hada Kai Don Magance Matsalar Sauyin Yanayi Tare

2023-12-14 19:58:51 CMG Hausa

Ranar 13 ga wata, shugaban tawagar kasar Sin, kuma mataimakin ministan kula da muhalli na kasar Sin Zhao Yingmin, wanda ya halarci taron kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar daidaita sauyin yanayi ta MDD karo na 28 wato COP28, ya gabatar da jawabi a yayin bikin rufe taron. Ya bayyana cewa, kasar Sin tana kira ga kasashen duniya da su hada kai, don magance matsalar sauyin yanayi cikin hadin gwiwa.

Zhao Yingmin ya ce, dan Adam yana da duniya guda daya ce kawai. A yayin da ake fuskantar matsalar sauyin yanayi a duniya, tilas ne kasashen duniya su hada kai, don daukar mataki tare, da yin Allah wadai da matakai na kashin daya da ke kawo tsaiko ga kokarin magance matsalar sauyin yanayi a duniya. Kasar Sin za ta himmantu wajen gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil’Adama, da cika alkawuran da ta dauka, da sa kaimi ga aiwatar da yarjejeniyar Paris, da tabbatar da aiwatar da dabarun raya kasa don tinkarar sauyin yanayi, da raya makamashi mai tsafta, da ba da gudummawa ga tsarin yanayi na duniya.

Bugu da kari, Zhao Yingmin ya bayyana cewa, kasashen da suka ci gaba suna da wani nauyi na tarihi da ba za a iya musantawa ba game da sauyin yanayi, don haka tilas ne su jagoranci rage fitar da hayaki mai yawa da kuma cimma burin rage fitar da hayakin kwata-kwata cikin sauri bisa tushen da ake bukata, tare da ba da goyon bayan da ya dace ga kasashe masu tasowa, don samun ci gaba mai dorewa.(Ibrahim)