Jami’in MDD ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su goyi bayan bukatun ‘yan gudun-hijira
2023-12-14 11:09:47 CMG Hausa
Babban kwamishinan kula da harkokin ‘yan gudun-hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi, ya bayyana fatan cewa sassan kasa da kasa, za su karfafa hadin-gwiwa, domin tabbatar da ‘yan gudun-hijira su samu kulawa, da goyon-baya yadda ya kamata.
Mista Filippo Grandi, ya jaddada hakan ne a yayin dandalin tattaunawa kan harkokin ‘yan gudun-hijira na duniya a jiya Laraba, inda ya ce akwai yankuna, ko kasashe daban-daban, wadanda a yanzu haka suke fuskantar babbar matsalar jin-kai da ‘yan gudun-hijira, ciki har da zirin Gaza, da Sudan, da Siriya, da Afghanistan.
Ya ce dalilin da ya haddasa akasarin matsalolin da suka ki ci suka ki cinyewa a duniya shi ne, sabani tsakanin bangarori da ba sa ga maciji da juna, da gazawar kasashe masu fada-a-ji, wajen samar da mafitar warware rikici ta hanyar siyasa. (Murtala Zhang)