logo

HAUSA

Yan bindiga sun harbe mutane 6 a kudancin Najeriya

2023-12-14 10:15:12 CMG Hausa

Rundunar sojojin Najeriya ta ce wasu ‘yan bindiga sun harbe mutane 6 ciki har da sojoji 4, tare da yin awon gaba da ‘yan Koriya ta kudu 2, lokacin da suka kai hari kan ayarin motocin da ke dauke da ma’aikatan kamfanin mai na Daewoo na kasar Koriya ta kudu, a kan titin Ahoada zuwa Abua dake jihar Rivers mai arzikin mai dake kudancin kasar.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, kakakin runduna ta 6 ta sojin kasar Danjuma Jonah Danjuma, ya ce ‘yan bindigar sun kaddamar da harin ne da safiyar Litinin, kuma ‘yan Koriya ta kudun da aka yi garkuwa da su, na tare da jami’an tsaro dake yi masu rakiya.

Danjuma ya kara da cewa, baya ga sojoji 4 da ‘yan bindigar suka hallaka, sauran fararen hula 2 da suka harbe, direbobi ne da kamfanin na Daewoo ya yi hayar su.

Jami’in ya ce akwai karin ma’aikatan mai 2 da suka bace yayin farmakin, kuma maharan sun yi nasarar tserewa ta cikin kogi bayan aikata wannan ta’asa. To sai dai kuma tuni jami’an tsaro suka bazama, domin tabbatar da cafke bata-garin, yayin da kuma ake ci gaba da laluben sauran mutane biyu da suka bace. (Saminu Alhassan)