logo

HAUSA

Kasashen Afirka na kara azamar kafa cibiyoyin hada hadar kudi na nahiyar

2023-12-14 10:42:06 CMG Hausa

An bude taron tuntuba, na sassa masu ruwa da tsaki daga kasashen Afirka, domin nazartar matakai, da tsare tsaren da ya kamata a yi, don kafa muhimman cibiyoyin hada hadar kudade na nahiyar Afirka.

Taron na yini 3 wanda aka bude a jiya Laraba, ya hallara wakilai daga ma’aikatun kudi, da manyan bankunan kasashen Afirka, da na hukumomin kungiyar AU, da jami’ai daga sassan raya tattalin arzikin yankunan nahiyar, da kuma abokan hadin gwiwar samar da ci gaba.

Ana sa ran taron zai mayar da hankali ga warware kalubalen tattalin arziki da na siyasa, da suka yiwa kasashen nahiyar tarnaki, wajen sanya hannu, da amincewa da tsare tsaren doka da suka wajaba a aiwatar kafin kafa cibiyoyin hada hadar kudaden na nahiyar Afirka.

Dokar kungiyar tarayyar Afirka ta AU mai nasaba da batun, ta tanadi kirkiro cibiyoyin hada hadar kudade na nahiyar Afirka 3, wato babban bankin Afirka, da asusun lamuni na Afirka, da kuma bankin zuba jari na nahiyar.  (Saminu Alhassan)