Taron raya tattalin arzikin kasar Sin ya kara shaida muhimmancin zuba jari a kasar
2023-12-14 12:45:57 CMG Hausa
A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, yadda Sin ta tsara manufofinta na raya tattalin arziki yana jawo hankalin duk duniya.
A wajen taron kolin raya tattalin arzikin kasar da ya gudana daga ranar 11 zuwa 12 ga watan Disambar nan, an tabbatar da wasu manyan fannoni 9, na habaka tattalin arzikin kasar Sin a shekara mai zuwa, ciki har da tsayawa ga raya tattalin arziki ta hanyar da ta dace, da karfafa tushen raya tattalin arziki, da kuma inganta farfadowar tattalin arziki da sauransu.
Hakan na nufin cewa, wannan taro ya kafa alkibla ga ayyukan raya tattalin arzikin kasar Sin a shekara mai kamawa, al’amarin da ya baiwa kasa da kasa damar kara fahimtar kokarin kasar na farfado da tattalin arzikin duk duniya bisa habaka tattalin arzikin kanta.
Taron ya kuma bullo da wasu ingantattun matakai na fadada bude kofa ga kasashen waje, wadanda suka shaida niyyar kasar Sin a fannin raya budadden tattalin arzikin duniya, ciki har da sassauta shingayen da aka kafa ga shiga kasuwannin sadarwa da kiwon lafiya, da bin ka’idojin tattalin arziki da kasuwanci na kasa da kasa, da tabbatar da aiwatar da wasu matakai 8 na raya shawarar “ziri daya da hanya daya” a zahirance. Da wannan muna iya fahimtar babban dalilin da ya sa yawan sabbin kamfanonin da baki ‘yan kasuwa suke zuba jari a cikin su a kasar Sin sun karu da kaso 32.1% a watanni 10 na bana. Kaza lika kasar Sin dake fadada bude kofa ga kasashen ketare, zabi ne mafi kyau ga kasashe daban-daban wajen raya kasuwanci. (Murtala Zhang)