logo

HAUSA

Jami’in Sin: Yarjejeniyar Paris ta sanya dan ba ga matakin farko na tantance yanayin da duniya ke ciki

2023-12-14 11:20:04 CMG Hausa

Shugaban tawagar Sin dake halartar taron kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar sauyin yanayi ta MDD karo na 28 wato COP28, kuma mataimakin ministan ma’aikatar kare muhallin kasar Sin Zhao Yingmin, ya bayyana a jiya Laraba cewa, yarjejeniyar Paris ta tantance yanayin da duniya ke ciki a karo na farko, kana ta aike da sako mai inganci ga al'ummar duniya, kuma tana da ma’ana mai muhimmancin gaske, kaza lika ta bude sabon babi game da batun yanayin duniya.

Bayan tattaunawa da aka gudanar sau da yawa a cikin mokonni 2 da suka gabata, taron ya cimma “matsaya daya ta Hadaddiyar Daular Larabawa” a kan abubuwan da yarjejeniyar Paris ta shafa, kamar tantance yanayin da duniya ke ciki a karo na farko, da rage sauri, da samar da daidaito, da jari, da tabarbarewa da sauransu.

Bisa kamalan Zhao Yingmin, bangaren Sin na ganin cewa, taron ya tabbatar da hasashen da aka yi. Har ila yau, tantance yanayin da duniya ke ciki a karo na farko, ya bude sabon babi game da batun yanayin duniya, ya yi bitar nasarori, da guraben da aka samu, kana ya kara karfafa sauye-sauyen kiyaye muhalli, da karancin carbon da ba za a iya jurewa a duniya ba, tare da nuna hanyar da za a bi a nan gaba, da kuma aikewa da sako mai inganci ga kasashen duniya, wanda hakan muhimmin ci gaba ne. (Safiyah Ma)