logo

HAUSA

Rundunar tsaron Najeriya ta ce babban aikinta shi ne kare al’umma da ’yan cin kasa sabanin yadda wasu ke kallon ta

2023-12-14 09:35:23 CMG Hausa

Rundunar tsaron Najeriya ta kara nanata cewa, ba burinta ba ne cutar da al’umma ko cin amanar kasa, aikinta shi ne tabbatar da tsaron kasa da kare rayukan ’yan kasa sabanin yadda wasu tsiraru ke yi mata munmunar fahimta.

Babban hafasan tsaron Najeriya Janaral Christopher Musa ne ya tabbtar da hakan jiya Laraba, 13 ga wata lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin majalissar wakilai kan kasafin kudi domin kare kasafin kudin hedikwatar tsaron kasar na shekara ta 2024.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.//////

Janaral Christopher Musa ya ce, kaddara tana iya fadawa kan kowane abu kuma a kowane lokaci, a don haka bai kamata wasu ’yan Najeriya su fara yanke kauna ga dakarun tsaron kasar ba a kan abun tsautsayi da ya faru a Kauyen Tudun Biri dake cikin jihar Kaduna wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula da dama.

Babban hafan tsaron na Najeriya yana wannan bayani ne bayan da ’yan kwamitin kasafin kudin suka bijiro da maganar jim kadan da kammala kare kasafin kudin hedikwatar tsaron kasa.

Ya ce, akwai kalubale a dukkan bangarori na tsaro, kuma suna bakin kokarin yin aiki tare da dukkan hukumomin tsaron Najeriya wanda suka hada da rundunar sojin sama waje shawo kan wadannan jerin kalubale.

“Al’amarin da ya faru a jihar Kaduna kuskure ne ba wai da gangan hakan ya faru ba, kuma muna daukar matakai na tabbatar da ganin cewa hakan ba zai sake faruwa ba, mun kasance a wannan matsayi ne dai domin mu kare al’umma amma ba don mu kashe su ba, muna matukar nadama da wannan al’amari, kuma muna tabbatar wa majalissar dokoki ta kasa cewa, za mu kara ba da himma ga aikinmu har sai al’ummar sun samu natsuwa da ’yan cin walwala tare da tabbatar da ganin cewa babu wata barazana ga rayuwa da kuma dukiyoyin al’umma a Najeriya.”

A jawabinsa shugaban kwamitin tsaro a majalissar wakilan ta tarayyar Najeriya Hon Babajimi Benson ya tabbatarwa hedikwatar tsaron ta Najeriya cewa, majalissar za ta bayar da dukkannin gudumawar da ta kamata wajen yaki da matsalar tsaro a kasa baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)