’Yan Republican sun kada kuri’a don binciken tsige Joe Biden
2023-12-14 10:15:43 CMG Hausa
A jiya Laraba ne ’yan majalisar wakilai na Amurka na jam’iyyar Republican suka kada kuri’ar amincewa da binciken tsige shugaban kasar Amurka Joe Biden, a kuri’u 221 da 212 da jam’iyyar ta kada, wanda ke nazarin ko Biden ya ci gajiyar harkokin kasuwancin waje na dansa Hunter Biden.
“Ikon tsige shi ya rataya a wuyan majalisar wakilai” kamar yadda shugaban kwamitin shari’a na majalisar Jim Jorda, wani mai tsaurin ra’ayi a jam’iyyar Republican, ya shaida wa manema labarai.
’Yan jam’iyyar Republican suna fatan kuri’ar neman tsigewar za ta ba su babbar dama bisa doka na kama dan shugaban kasa wato Hunter Biden idan bai gabatar da kansa a gaban majalisar ba.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kwakkwarar hujja da ta bayyana da ke nuna cewa Joe Biden, a matsayinsa na shugaba a yanzu ko a baya, ya yi amfani da ikonsa ba bisa ka’ida ba ko kuma ya karbi kudaden haram. Duk da haka, akwai damuwa ta da’a game da harkokin kasuwancin kasa da kasa na dangin Biden. (Yahaya)