logo

HAUSA

Amurka za ta ba da karin taimakon soja na dallar Amurka miliyan 200 ga Ukraine

2023-12-13 11:01:45 CMG Hausa

Jiya Talata, fadar White House ta Amurka, ta fitar da sanarwa dake cewa, shugaban kasar Joe Biden ya gana da takwaransa na kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy, inda ya bayyana jerin matakan da kasar Amurka za ta dauka domin ba da taimakon tsaro ga kasar Ukraine, ya kuma jaddada cewa, ya kamata majalisar dokokin Amurka ta dauki matakan gaggawa, ta yadda za a tabbatar da goyon bayan kasar Ukraine a fannin kare tsaron kasar yadda ya kamata.

A taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar, Joe Biden ya ce, kasar Amurka za ta ci gaba da samar da muhimman makamai, da kayayyakin soja ga kasar Ukraine, inda ya kuma zartas da kudurin samarwa Ukraine makamai masu linzami na tsaron sama, da manyan bindigogin harba boma-bomai, da kuma harsasai da sauransu, wadanda darajarsu za ta kai dallar Amurka miliyan 200.

Kafin hakan, kasar Rasha ta sha jaddada cewa, matakin kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya na ci gaba da samar da makamai ga kasar Ukraine, da rura wuta a tsakanin kasashen biyu, zai haddasa karin barazana ga kasar Ukraine, da kuma karin asarar rayuka, da jikkatar al’ummun kasar. (Maryam)