logo

HAUSA

Najeriya za ta kara adadin kudaden da take warewa bangaren kiwon lafiya a kasafin kudin 2024

2023-12-13 09:21:18 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa, gwamnatinsa za ta dora fifikon gaske kan sha’anin kiwon lafiya ta hanyar kara adadin kason da ake warewa bangaren a cikin kasafin kudin shekarar badi ta 2024.

Ya tabbatar da hakan ne ranar Talata, 12 ga wata a birnin Abuja lokacin da ya jagoranci bikin sanya hannnu kan yarjejeniyar ayyukan hadin gwiwa a fannin lafiya tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da kuma sauran hukumomin agajin kiwon lafiya na kasa da kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, gwamnatinsa ba za ta yi da wasa ba wajen saka jari mai yawan gaske a kan sha’anin kiwon lafiya, kasancewarsa jigo daga cikin jerin kudurce-kudurcen gwamnati.

Gangamin taron sanya hannu yana daga cikin wani bangare na bikin ranar kula da lafiya ta duniya wanda kuma ake gudanarwa a ranar 12 ga watan Disambar kowace shekara.

Shugaban na tarayyar Najeriya ya bayyana cewa, gwamnati za ta sake fasalin tsare-tsarenta na kiwon lafiya ta fuskar samar da kayan aikin jinya da tsarin horas da ma’aikatan lafiya wanda za a fara kuma daga shekara mai zuwa ta 2024, kuma za a cimma hakan ne tare da hadin gwiwa da daukacin jihohin kasar 36 na kasar.

A game kuma da batun tsadar neman lafiya da al’umamr kasar ke fuskanta kuwa, shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ce, za a inganta tsarin asusun kula da kiwon lafiya na kasa domin tabbatar da ganin an bunkasa damarmakin dake tattare da asusun kamar dai yadda aka tsara a cikin dokar kiwon lafiya ta kasa ta 2014.

Bikin dai ya sami halartar dukkannin gwamnonin jihohin kasar da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki a kan sha’anin kiwon lafiya daga dukkan matakai. (Garba Abdullahi Bagwai)