logo

HAUSA

Dokar tsaron kasa ta yi kyakkyawan tasiri a yankin Hong Kong

2023-12-13 17:08:58 CMG Hausa

Sanin kowa ne cewa, kiyaye tsaron kasa, batu ne da ya shafi muhimman muradun kowace kasa a duniya. Kuma tun bayan da yankin musamman na Hong Kong ya dawo karkashin ikon kasar Sin, bisa ka'ida ta 23 cikin babbar dokar yankin, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta dankawa yankin izinin kafa dokarsa ta fannin kiyaye tsaron kasa.

Sai dai kafin kafa dokar, yankin ya fuskanci wasu ayyuka na rashin doka a bangaren tsaron kasa wanda masana ke cewa, ba ya rasa nasaba da tsoma baki a harkokin yankin daga ketare.

Idan ba a manta ba a shekarar 2019, wasu bata-gari suka yi yunkurin balle Hong Kong daga kasar Sin, da cin zarafi gami da lalata tambari da tutar kasa, da zuga al'umma don su mamaye ofishin gwamnatin tsakiya dake Hong Kong, da kai hari kan mai uwa da wabi, da cin zarafin ’yan sanda wadanda a kullum suke sadaukar da rayukansu don tabbatar da tsaron al’umma, al'amuran da suka kasance ayyukan ta'addanci, da haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a Hong Kong gami da cikakken iko na kasa.

Kuma duk wata kasa da ta san abin da take yi, ba za ta amince da irin wannan danyen aiki ba. Bayan kafa wannan doka, a makon nan aka yi nasarar gudanar da zaben ’yan majalisar kafa dokoki ta yankin Hong Kong karo na 7. Wannan shi ne zaben ’yan majalisar kafa dokoki ta yankin karo na farko, tun bayan aiwatar da manufar "tabbatar da ’yan kishin kasa su yi mulkin yankin Hong Kong", da kuma sake fasalin tsarin majalisar kafa dokokin yankin.

Masharhanta na ganin cewa, yankin Hong Kong ya dauki kwakkwaran mataki, na tafiyar da harkokin yanki yadda ya kamata. Yanzu haka dai, an zabi mambobin kwamitocin gundumomin mazabu 176, da kuma kansilolin mazabu 88, matakin dake kara tabbatar da muhimmancin dokar tsaron kasa da aka kafa a yankin.

Kuma tun lokacin da aka kafa, tare da fara aiwatar da dokar tsaron kasa mai nasaba da yankin Hong Kong, wadda wata muhimmiyar dama ce ta yanke hukunci ga baragurbin dake neman ta da rikici a yankin, lamarin da ya tabbatar da ci gaba mai dorewa a yankin, da ma tafiyar da tsarin nan na kasa daya amma tsarin mulki iri biyu yadda ya kamata.

Jagororin yankin dai sun sha nanata cewa, masu bin doka suna maraba da dokar tsaron da aka kafa, matakin da ya kara janyo masu sha’awar zuba da neman halaliya tare da kara dawo da martabar yankin a idon duniya.

Yanzu dai yankin Hong Kong ya zabi ’yan majalisu masu kishin kasa, wadanda za su kara janyowa yankin martaba da wadata. Matakin da masu sharhi ke cewa, ya bude wani sabon babi a yankin, tun bayan da aka kafa sabbin dokokin tsaron kasa da na zabe masu alaka da yankin. (Ibrahim Yaya)