Babban taron MDD ya zartas da kudurin tsagaita wuta a Gaza
2023-12-13 10:10:32 CMG Hausa
A jiya Talata 12 ga wata ne aka kira taron gaggawa na musamman a zauren MDD, inda aka zartas da wani kuduri dake bukatar a tsagaita bude wuta a zirin Gaza bisa dalilan jin kai. Kudurin ya samu kuri’un amincewa daga kasashe 153, da kuri’un adawa daga kasashe 10, tare kuma da wadanda suka janye jiki daga kasashe 23.
Kudurin ya nuna damuwa matuka game da yanayin jin kai mai tsanani da zirin Gaza ke ciki, da wahalhalun da Palasdinawa fararen hula ke fuskanta, kuma an jaddada cewa, ya zama wajibi a kare fararen hula na Palasdinu da Isra’ila bisa dokar jin kai ta kasa da kasa.
Don haka kudurin ya bukaci a tsagaita bude wuta a zirin Gaza nan take, kuma a saki mutanen da aka tsare ba tare da gindaya kowanen sharadi ba, kana a tabbatar da gudanar da ayyukan samar da taimakon jin kai.
Haka zalika, kudurin ya amince da jingine gudanar da taron gaggawa na musamman karo na 10, game da rikicin Palasdinu da Isra’ila na dan lokaci, ya kuma mika wa shugaban babban taron MDD ikon sake kiran taron bisa bukatun kasashe mambobin majalisar.
A nasa bangaren, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya yi maraba da kudurin da aka zartas da shi yayin babban taron MDD bisa kuri’u masu rinjaye, yana ganin cewa, lamarin ya nuna yunkurin al’ummun kasa da kasa kan batun, shi ya sa dole ne a aiwatar da kudurin daga fannoni. Zhang Jun ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da taka rawar gani, ta yadda za a maido da zaman lafiya da ceton rayuka da kuma sassauta rikicin jin kai a wurin a kan lokaci. (Jamila)