logo

HAUSA

MDD: Adadin masu fama da yunwa a tsakiya da yammacin Afirka zai kai mutum miliyan 49.5 a shekarar badi

2023-12-13 10:54:02 CMG

Sakamakon wani nazari na MDD, ya nuna yadda adadin masu fama da kamfar abinci a yankunan tsakiya da yammacin Afirka ke karuwa, adadin da nazarin ya yi hasashen na iya kaiwa mutum miliyan 49.5 ya zuwa tsakiyar shekarar 2024 dake tafe.

Da yake bayyana hakan a jiya Talata, kakakin babban magatakardar MDD Stephane Dujarric, ya ce adadin masu fama da yunwa a yankunan 2 na iya kaiwa hasashen da aka yi tsakanin watan Yuni da Agustan shekarar ta badi.

Nazarin ya nuna cewa, yunwa na kara kamari musamman a kasashen dake iyaka da teku, inda adadin mata, da maza da yara kanana dake fama da matukar kamfar abinci, ka iya kaiwa miliyan 6.2, wato karuwar kimanin kaso 16 bisa dari a bana.

Ana alakanta matsananciyar yunwa a wadannan yankuna ne da aukuwar tashe-tashen hankula, da mummunan tasirin sauyin yanayi, da kuma tashin gwauron zabin farashin abinci da man fetur.   (Saminu Alhassan)